January 17, 2023
An Yi Zaman Tattaunawa Kan Halin Da Yemen Ke Ciki

Wani babban jami’in gwamnatin Houthi a Yemen, ya ce tattaunawar da aka yi da wakilan gwamnati da kuma Saudiyya wanda kasar Oman ta jagoranta, ta fara share hanyar maido zaman lafiya a kasar.
Abdul Salam ya shaidawa gidan talbijin din kasar cewa, sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi ayyukan jin kai, da yadda za a kai agaji ga dubban ‘yan kasar da ke tsananin bukatar taimako.
Tun shekarar 2014 kasar Yemen ta fada yakin basas, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubun dubatar mutane cikin shekaru kusan 10, yayin da wasu sama da miliyan hudu sukayi gudun hijira wasu kasashe makofta.