May 13, 2023

An Yi Tattaunawa Ta Wayar Tarhon A Tsakanin Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Iran Da Saudiyya

 

Ministocin harkokin kasashen wajen na Iran da Saudiyyar sun tattauna matsaya ta karshe dangane da yarjejeniyar da su ka kulla a birnin Beijin na kasar China.

Ministan harkokin wajen na Iran Hussain Amir Abdullahiyan ya bayyana wa takwaransa na Saudiyya gamsuwarsa akan inda aka kwana na aikewa da tawagar kwararru da dukkanin kasashen biyu su ka yi domin duba yadda ofisoshin jakadancinsu suke ciki.

Shi ma Ministan harkokin wajen Saudiyya ya bayyana jin dadinsa aka halin da ake ciki na kyautatuwar alaka a tsakanin kasashen biyu

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An Yi Tattaunawa Ta Wayar Tarhon A Tsakanin Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Iran Da Saudiyya”