May 26, 2023

An yi kira da a cimma burikan bai daya na raya nahiyar Afrika

Nahiyar Afrika ta yi bikin ranar Afrika da ake yi kowacce shekara a jiya Alhamis, inda aka yi kira da a tabbatar da cimma burikan raya nahiyar.
Ana bikin ranar Afrika ne a ranar 25 ga watan Mayun kowacce shekara, domin jinjinawa nasarorin da kungiyar tarayyar Afrika OAU da yanzu ta zama AU, ta samu tun bayan kafuwarta a makamanciyar ranar a shekarar 1963.
An gudanar da biki na musammam mai taken “Afrikarmu, Makomarmu”, a hedkwatar Tarayyar Afrika dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, domin murnar cika shekaru 60 da kafa kungiyar.
Da yake jawabi, shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat, ya jaddada bukatar hada karfi da karfe wajen cimma burikan da suka assasa kafa kungiyar tarayyar Afrika ta OAU da ma burikan da AU ke da su a yanzu.
A nasa bangare, shugaban kasar Comoros, Azali Assoumani, dake shugabantar AU a wannan karo, ya yi kira ga daukacin al’ummar nahiyar daga dukkan bangarori, su hada hannu wajen inganta ci gaban nahiyar tare da tabbatar da cikar burin bai daya na samun ci gabanta.
Shi kuwa firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed, ya nanata bukatar amfani da albarkar jama’a da sauran albarkatun kasa da nahiyar ke da su, wajen cimma ajandar samar da ci gabanta.

(Fa’iza)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An yi kira da a cimma burikan bai daya na raya nahiyar Afrika”