An yankewa Dan sandan da ya kashe Lauya hukuncin kisa a jihar Legas

Rahotanni daga jihar Legas na bayyana cewa Mai Shari’a Ibironke Harrison na babbar kotu a jihar ta yankewa wani mataimakin Sufurtandan ‘Yan sanda ASP Drambi Vandi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kisan wata Lauya mai suna Omobolanle Raheem wacce take dauke da juna biyu.
Gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da ASP Vandi a gaban Kotu ne a watannin baya, inda take tuhumarsa da laifin harbin ma’aikaciyar Lauyar mai kimanin shekaru 41 a yankin gadar Ajah ranar 25 ga watan Disambar bara.
Lamarin da ya bar baya da kura tsakanin al’umma musamman a shafukan sada zumunta wanda hakan ta kai ga dakatar da wanda ake tuhuma da laifin daga hukumar yan sanda.
A karon farko dai an zargi ASP Vandi da laifin kisan kai, sai dai kuma daga baya aka sassauta zargin bisa hujjojin da ke nuna ya aikata hakan ne bisa kuskure.
A yayin sauraron karar, wanda ake tuhuma ya gabatar da shaidu guda 11 kana inda ya yi ikirarin cewa abinda ya aikata cikin kare kansa yayi hakan.
Sai dai daga bisani Alkali ta bayyana shi matsayin wanda ya aikata laifin kisa bisa hujjojin da Lauyoyi suka gabatar don bibiyar hakkin wacce aka kashe.