April 1, 2024

An yanke wa dan adawar kasar CAR hukunci bisa laifin bata suna


An yanke wa daya daga cikin manyan ‘yan adawa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya hukuncin daurin shekara guda a gidan yari bisa samunsa da laifin bata suna da kuma raina kotu.

Crepin Mboli Goumba, lauya kuma kodineta na kungiyar adawa ta BRDC, an kama shi ne a farkon wannan watan bayan ya zargi alkalai da cin hanci da rashawa.

An umarce shi da ya biya tarar kusan dala 130,000. Masu gabatar da kara sun nemi daurin shekara daya a gidan yari. Lauyoyinsa sun ce za su daukaka kara kan hukuncin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

#CARAR

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An yanke wa dan adawar kasar CAR hukunci bisa laifin bata suna”