January 16, 2023

An Shiga Farautar Matan Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Burkina Faso

 

Bayanai daga Burkina Faso, na cewa an shiga neman gungun matan da ake kyautata zaton ‘yan bindiga sun sace a karamar hukumar Arbinda dake yankin Sahel.

A halin dake ciki dai babu tabbataccen adadi na yawan matan da ake sace.

Saidai wata majiyar soji ta shaidawa masu aiko da rahotanni cewa mata kimanin 48 ne ‘yan bindigan suka sace.

Matan sun je neman ruwan sha ne a yankin, kamar yadda wasu 4 daga cikinsu da suka tsere suka shaida.

Majiyoyin daga yankin na kyatata zaton mayakn jihadi ne suka sace matan kuma a lokuta guda biyu, tun daga ranar Alhamis.

Yankin Arbinda dai ya jima dake karkashin barazanar mayaklan dake ikirari da sunan jihadi.

©Hausatv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An Shiga Farautar Matan Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Burkina Faso”