Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

July 28, 2021

AN SAUYAWA MANYAN JAMI’AN ƳAN SANDA 24 WURAREN AIKI

AN SAUYAWA MANYAN JAMI’AN ƳAN SANDA 24 WURAREN AIKI

 

 

Babban sufeton ƴan sandan Nijeriya Usman Alƙali Baba, ya ba da umarnin yin sauyin wararen aiki ga wasu jami’an masu muƙamin mataimakan sufeto janar 24.

 

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da rundunar ƴan sandan ta fitar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunta na ƙasa Frank Mba.

 

Sanarwar ta ruwaito ycewa tsohon Kwamishinan ƴan sandan birnin tarayya Abuja Bala Chiroma, da aka ɗaga likkafarsa zuwa mataimakin sufeto janar, an mayar da shi shiyya ta 7 da ke Abuja.

 

Sannan Dasuki Galadanci, da aka mayar da shi shiyya ta 17 da ke Akure a Jihar Ondo.

 

Haka kuma sanarwar ta ce, sauyin wuraren aikin ya fara aiki ne nan take.

 

SHARE:
Labaran Duniya One Reply to “AN SAUYAWA MANYAN JAMI’AN ƳAN SANDA 24 WURAREN AIKI”
Ahlul Baiti
Ahlul Baiti

COMMENTS

One comment on “AN SAUYAWA MANYAN JAMI’AN ƳAN SANDA 24 WURAREN AIKI

    Author’s gravatar

    Wai Daman har yanzu sokojin America basu Kare a Iraq ba?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *