January 16, 2023

An Samu Habakar Man Da Iran Ke Fitarwa Duk Da Takunkuman Amurka

Man da Iran ke fitarwa ya kafa tarihi, a watan Nuwamba da Disamban shekarar data gabata, wannan kuwa duk da takunkuman da Amurka ta kakabawa gwamnatin Tehran.

Bayanai sun nuna cewa wannan baya rasa nasaba da yadda Iran da Sin, suka kara karfafa alakarsu ta tattalin arziki a shekarar data shude.

Dama dai Sin, ta kasance babbar kawa ta fuskar kasuwanci da kasuwanci kuma babbar mai sayan man fetur din na Iran.

A bayannin da kwararu na kasuwancin man fetur na Kpler suka fitar, Iran ta fidda gangar danyen man fetur miliyan 1, 23 a ko wace rana a watan Nuwamba bara, kusan yadda yake idan aka kwatanta da shekarar 2019.

An kiyasta cewa man da Sin ta shigo da shi daga Iran a watan Disamba shi ma ya kafa tarihi zuwa miliyan 1,2 a watan Disamba da ya gabata, kwatankwacin karin kashi 130% a shekara guda.

Saidai a hukumance China na daukar man fetur din na Iran a matsayin wanda ya shigo daga wasu kasashe domin kaucewa matsaloli da Amurka.

Baya ga Sin, ma Iran na fitar da gurbatacen man fetur zuwa kasar Venezuela inda take tace shi.

 

©Hausa tv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An Samu Habakar Man Da Iran Ke Fitarwa Duk Da Takunkuman Amurka”