January 10, 2024

An sake zaben shugaban Kongo Kinshasa Felix Tshisekedi

Kotun tsarin mulkin Kongo Kinshasa ta yanke hukuncin da ya tabbatar da sakamakon babban zaben da aka gudanar kwanan nan da yammacin jiya Talata, inda aka sake zaben shugaban kasar Felix Tshisekedi.

Kwamitin zaben kasar ya sanar da cewa, yawan kuri’u yayin babban zaben na wannan karo ya kai kashi 43 cikin dari. Bisa jadawalin babban zabe, sabon shugaban kasar zai sha rantsuwar kama aiki a ranar 20 ga watan Janairu.

Bisa dokar zabe, ana gudanar da babban zabe ne bayan kowane shekaru biyar-biyar. Kana an amince da tsarin zabe zagaya daya, wato wanda ya sami kuri’u mafi yawa shi ne ya yi nasarar cin babban zaben kasar.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An sake zaben shugaban Kongo Kinshasa Felix Tshisekedi”