February 8, 2023

An Sake Gano Wani Banki Da Ya Boye Sabbin Kudi Sama Da Naira Milyan 200

A wani bangaren kuma, Hukumar Yaki da Cin hanci da karbar Rashawa ta sake bankado wat naira milyan 258 da aka boye a wani banki, a yayin da ake tsaka da fama da matsalar rashin kudi a hannu a kasar nan.

 

Kakakin hukumar, Azuka   Ogugua  ya  ce  kudin da jami’an  hukumar  suka  gano  sabbi  ne baki dayansu ,  Inda  aka  samu  kudin a  cikin   bankin   Sterling.

Ya  kara da cewa  Babban bankin kasa ne ya  saki  kudin  domin  a  rarraba  su  ga abokan  huldar bankuna, amma  bankin   ya   boye  su.

Hakan na  zuwa  ne  kasa  da kwana  daya  bayan da Manajan wani banki  ya  fada  komar  hukumar  EFCC  a Abuja  bisa  zarginsa  da kin  raba   sabbin kudi  har naira  milyan  29  ga abokan  huldar  bankin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An Sake Gano Wani Banki Da Ya Boye Sabbin Kudi Sama Da Naira Milyan 200”