October 7, 2021

An sace mutane 4 a jahar Ekiti, ‘Yan sanda sun yi nasarar ceto 1 daga cikin su

Daga Isah Musa Muhammad


‘Yan bindiga sun sace manoma 3 tare yaro guda a jiya Laraba da tsakiyar-dare a Ilasa dake yanki karamar hukumar Ekiti ta gabas.

Wani shaidan gani-da-ido ya tabbatar da cewa yan bindigan sun zo ne da dare misalin karfe 1:30 inda suka kutsa yankin gidajen gona a Eti-Ero suka fara harbi wanda hakan ya sanya watsewar jama’ar da ke wurin inda wasu suka nufi daji don neman tsira da rayukan su.

Shigar yan bindigan ke da wuya suka fara bincika gidaje, inda anan ne suka kama wani yaro dan kasa da shekaru 10 da kuma wasu manoma guda 3 kana suka yi awun gaba da su.

Saidai kuma jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandam ASP Sunday Abutu ya bayyana cewa mutane 2 ne aka yi garkuwa da su ba 4 ba, ya kuma ce sun yi nasarar ceto daya daga mutane biyun kana kuma sun damke wani mutum da ke da hannu a faruwar lamarin.

Ya ce zuwa yanzu jami’an su na bincika dazukan ketare don gano inda aka ajiye mutum 1 da ya rage din.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An sace mutane 4 a jahar Ekiti, ‘Yan sanda sun yi nasarar ceto 1 daga cikin su”