September 6, 2021

An Sace Basarake A Neja

Daga Muhammad Bakir Muhammad

 

Wasu mutane da ake zargin yan bindiga ne sun sace wani basarake na masarautar Borgu dake jahar Neja mai suna Dr. Mahmud Ahmed Aliyu.

Rahotanni sun nuna cewa an sace shi ne daga Fadarsa da misalin karfe 9 na dare a Wawa yankin Sabuwar Bussa shalkwatan karamar hukumar Borgu dake jahar Neja.

Wata majiya ta nuna cewa yan bindigan sun kustsa cikin fadar tasa a kan babura har guda biyar inda kowanne babur ke dauke da mutane biyu inda suka cimma shiga ciki bayan nasara akan wasu tsirarun masu gadi a kofar.

Bayanai sun nuna cewa yayin shugar su sun tadda shi tare da wasu mutane da kuma iyalansa amma basu dau kowa ba sai shi kadai.

Yan bindigan dai sun dau Dr. Mahmud yayin da iyalansa ke kallo kana kuma sun dauke shi ba tashe da dukan sa ba balle cutar dashi. Kuma an bayyana cewa ya zuwa yanzu babu wani labari ko kiran waya daga wadanda suka dauke shi din.

Tuni dai aka samu karin bayani daga gurin mai magana da yawun yan sandan jahar, Wasiu Abiodun inda ya tabbatar da cewa zuwa yanzu suna kan tattara bayanai da kuma kokarin gano inda yan bindigan suka kai basaraken.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An Sace Basarake A Neja”