March 31, 2024

An Raya Daren Na Biyu daga Dararen “Lailatul-Qadari” A Najeriya

A jiya Asabat ne yan shia  a Najeriya su ka raya dare na Biyu  daga cikin dararen ‘lailatul-Qadari’ a cikin masallatai da wasu cibiyoyi na addini ta hanyar yin

karatun alkur’ani da yin adduo’i da salloli.

Da asubahin ranar 19 ga watan Ramadan ne dai wani Bakawarije, Ibn Muljim ya sari Imam Ali (a.s) da takobi a lokacin da ya yi sujjada yana limancin sallar asuba a masallacin Kufah. Takobin Ibn Muljim wacce take da guba ta yi wa Imam Ali raunin da shi ne ya yi sanadiyyar shahadarsa a ranar 21 ga watan Ramadan.

Mabiya mazhabar Ahlul Bayti ( a.s) a duniya suna raya wadannan dararen na 19, 21 da 23 ga watan Ramadan ne da karatun alkur’ani da kuma addu’oi da zummar neman gafara a wurin Ubangiji madaukakin sarki.

Daga cikin muhimman cibiyoyin da akayi aiyukan akwai sallatan Shia na  Rasulul a azam Dake dawanau a birnin Kano da pataskum da Hussainiyar Baqirul ulum dake Danbare da gayawa da markaz na yan,uwa musulmi a birnin Kano  da Cibiyoyin Rasulul a azam Dake garuruwan Bauchi, Gombe, misau, azare, katagum jama,are  Dass Maiduguri Pataskum,Damaturu,Katsina, Gusau, Sokoto, kebbi,Yawuri,Ngaske, Kaduna,Minna Neja, Abuja,Suleja, Dandume,Daura, Saminaka,Zariya,da wasu daruruwanan cibiyoyin shia Dake Najeriya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An Raya Daren Na Biyu daga Dararen “Lailatul-Qadari” A Najeriya”