September 15, 2021

An Rantsar Da Kwamishinonin INEC 3

Daga Muhammad Bakir Muhammad

 

Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari ya rantsar da kwamishinoni 3 na hukumar zabe ta kasa (INEC).

Kwamishinonin uku an rantsar da su ne kafin zama da ake gudanarwa a gidan gwamnati a dakin tattaunawa da ke gidan gwamnatin a garin Abuja.
Kwamishinonin 3 sun hada da Dr. Baba Bia mai wakiltan Arewa ta gabashi; Farfesa Sani Adam mai wakiltan Arewa ta tsakiya da kuma Farfesa Abdullahi Abdu mai wakiltan Arewa ta yamma.

 

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo, Magatakardan gwamnatin tarayya ta kasa, Boss Mustapha na daga mahalarta taron wanda aka fara wuraren karfe 9 na safiyar yau.
A tare dasu akwai mahalarta kamar su ministan al’adu, Lai Muhammed; Antoni Janar kuma ministan shari’a, Abubakar Malami da sauran mahalarta taron.
A bangare guda kuwa akwai ministan kudi da kasafi na kasa Zainab Ahmed, Ministan aiyuka Babatunde Fashola, Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbeshola.

 

Kana a wani bangaren kuma shugaban ma’aikata Folashade Yemi-Esan da sauran ministoci daga ofisoshi daban daban sun samu halartar taron.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An Rantsar Da Kwamishinonin INEC 3”