March 27, 2023

An Kashe ‘Yan sanda 2, Wasu Da Dama Sun Jikkata A Wata Arangama Da Sojoji A Taraba

 

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, SP Abdullahi Usman ya sanar da cewa, lamarin ya faru ne yayin da wani soja da ke binciken ababen hawa a wani titi da ke daura da Hedikwatar hukumar zabe INEC da ke Jalingo, ya tare wata jami’ar ‘yan sanda da ke aiki a INEC don yi mata bincike

A cewarsa, daga nan sai sabani ya shiga a tsakaninsu inda jami’ar ta wuce zuwa cibiyar tattara sakamakon zaben, sojan kuma ya bita ya fitar da ita da karfin tsiya sai rikici ya kaure.

Kakakin ya kara da cewa, a yanzu kwamishina Yusuf A. Suleiman da kwamanda na bataliya ta shida da ke Jalingo na kan tattaunawa kan lamarin inda suka amince da kafa kwamitin da zai yi bincike kan abin da ya jawo sabanin.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An Kashe ‘Yan sanda 2, Wasu Da Dama Sun Jikkata A Wata Arangama Da Sojoji A Taraba”