October 20, 2021

An kashe wasu masu sarautar gargajiya a jihar Imo

Daga Danjuma Makeri


Majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Imo ta fada cikin yanayi na alhini kan kisan wasu mutane 2 daga cikin mambobin ta.

Rahoto ya bayyana cewa mutanen biyu sun kasance suna halartar wani taro a Nnenasa dake karamar hukumar Njaba dake jahar Imo inda wasu yan bindiga suka kutsa cikin dakin taron.

Masu sarautar da suka rasa rayukan nasu sun hada da Eze E A Durueburuo wanda ya kasance Obi ne na Okwudor, da kuma Eze Sampson Osunwa wanda ya kasance daga yankin Ihebinowere.

Rahoton ya nuna cewa wasu da dama daga cikin sarakunan da suka halarci taron sun tsira da raunuka a jikin su.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar ta Imo, Mike Abattam ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce babu shakka mutum biyu sun rasa rayukan su ya kuma ce mutanen da suka jikkata an dauke su zuwa asibiti.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An kashe wasu masu sarautar gargajiya a jihar Imo”