September 15, 2021

An Kashe Shugaban ISWA; Al-Barnawi

Daga Muhammad Bakir Muhammad

______________________________________________________________________________________________

An samu nasarar hallaka shugaban kungiyar masu ta da kayan baya da rajin kafa gwamnatin musulunci a yammacin Afirka (ISWAP), Abu Musab Al-Barnawi. Ya zuwa yanzu hukumar sojin Najeriya bata yi cikakken bayani kan kisan nasa ba, amma rahotanni daga majiya daban daban sun bayyana cewa an kashe shi ne a satin da ya gabata cikin watan Augusta na wannan shekarar.

 

Shugaban kungiyar ta ISWAP dai ya kasance d’a ga tsohon shugaban kungiyar Boko Haram Mohammed Yusuf wanda jami’an tsaron Najeriya suka kashe shekaru 11 da suka gabata (2009) bayan kirkirar kungiyar Boko Haram da yayi kuma ya aiyana ta matsayin kungiya mai yaki da gwamnatin Najeriya da fafutukar kafa sabuwar gwamnati.

 

A shekarar 2016 yan ta’addan kungiyar “Daular Musulunci” (Islamic State) suka shelanta shugabantar da Al-Al-Barnawi matsayin wakilinta a yammacin Afirka da kasancewa Shugaban kungiyar Boko Haram wanda Abubakar Shekau ke jagotanta wanda ya kasance na jagotantar kungiyar tun bayan kisan Mohammed Yusuf.

 

Shekau ya kashe dubban rayuka da tarwatsa garuruwa da dama wanda hakan ya haifar da gudun hijira a sassan Arewa ta gabashin Najeriya, Shekau ya kula yarjejeniyar yin aiki da kungiyar IS ne cikin shekar 2015.

 

Tsige Shekau daga shugancin kungiyar Boko Haram ya haifar da rabuwar kungiyar zuwa tsagi biyu tare da hamayya da gaba tsakanin su.

 

An bayyana cewa tsige Shekau da kungiyar ISIS suka yi na da alaka da saba yarjejeniyar da suka yi da shi, a bangare guda kuma don su samu cikakken goyon bayan mayakan Boko Haram saboda kasancewa Al-Barnawi d’a ga wanda ya assasa kungiyar, bugu da kari kuma its kungiyar ta ISIS ta horas da shi Al-Barnawi kafin su danka masa wannan mukami.

 

Shekau, wanda ya kasance kasar Amurka ta bada umarnin gani da harbi kansa, da kuma sanya farashi mai yawa kan wanda ya nuna inda yake ko ya damka shi ga hukuma tun wancan lokacin ke boye a yankin dajin Sambisa da kuma bangaren dutsen Mandara dake makobtaka da kasar Kamaru.

 

Daga bangare guda kuwa Al-Barnawi ya kai hare-hare da dama kan jami’an tsaro a yankin tafkin Chadi kana kuma da dabarun kawar da Shekau.

 

Kana ya kasance yana da cikakken iko a arewacin Borno inda ya wajabta haraji kan mutane inda yake samun kudin shiga mai yawa bayan kudaden tallafi da yake samu daga kungiyar ISIS.

 

Ya kuma tarwatsa da yawa daga sansanin sojoji a garin Dikwa, Manguno, Abadam duk a jahar Borno, da kuma wasu sansani da garuruwa a yankin Geidam dake jahar Yobe.

 

Kana kuma ya samar da sansanoni a yankunan tafkin chadi don kai hare-hare akan sojojin Najeriya, Nijar da Chadi.

 

Bayan kisan Shekau a watan Mayu na 2021, watanni uku baya, rahotannin kisan Al-Barnawi ya karade shafukan sa da zumunta. Inda kisan nasa ake gani a matsayin babbar nasara ga kawo karshen ta’addanci a Najeriya. Bayan shafe shekaru a kalla 12 na rashin zaman lafiya a kasar.

 

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An Kashe Shugaban ISWA; Al-Barnawi”