October 7, 2021

An kashe mutane da kuma kona gidaje da dama a Zamfara

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Rahotanni daga Zamfara sun bayyana cewa a ranar Talatan da ta gabata ne yan bindiga suka kai hari yankin Kuryar Madaro da ke karamar hukumar Kauran Namoda na jahar Zamfara inda suka kashe mutane da dama cikin yan kauyen kana kuma suka cinna wuta a ababen hawa da gidaje.

 

BBC ta ruwaito cewa mazauna kauyen sun bada rahoton cewa yan bindigan sun farmaki kauyen ne da misalin karfe 10 na dare inda suka share tsahon lokaci suna aiwatar da farmakin.

Sun kuma kara da tabbatar da cewa yan bindigan sun kashe mutane 19, kana kuma sunyi awun gaba da kayan masarufi na abinci da kuma dabbobi.

Hukumar yan sandan jahar sun tabbatar da faruwar lamarin, kana kuma tace ta aika da jami’nata zuwa kauyen cikin gaggawa.

Kauyen na daya daga cikin yankunan da suka fuskanci katsewar layukan waya a jahar.

Wasu daga mazauna kauyen sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kona gidaje 13 da ababen hawa guda 16 inda suka bayyana cewa wasu daga ababen hawan mallakin hukumar yan sandan ne.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An kashe mutane da kuma kona gidaje da dama a Zamfara”