September 15, 2021

An Kashe Kwamandan Yan Banga A Jahar Kogi

Daga Muhammad Bakir Muhammad

 

Wani sananne daga sanannun kwamandojin yan banga mai suna Alhassan Alhassan, ya samu raunin harbi yayin musayar wuta da masu garkuwa da mutane wanda yayi sanadiyyar rasa ran sa.

Musayar wutan ya kasance A wani daji na yankin Tanahu, dake karkashin masarautar Gegu-Beki na karamar hukumar Kogi.
Wani daga jami’an yan bangan wanda ya kasance daya daga mutanen da lamarin ya ritsa da su ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar talata da misalin karfe 11:23 na safiya.

Ya bayyana cewa kwamandan ya jagotanci yaransa zuwa cikin dajin saboda fito-na-fito da masu garkuwa mutanen wanda suka kasance suna addabar yan kauyukan yankin Aduho da Tanahu.

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun yi musu kwanton bauna ne a yayin da suka hango su, babu zato ba tsammani sai suka far musu da ruwan harsasai masu rai.
Duk da suna harbin su ma sun yi kokari mayar da martani a yayin da musayar wuta ta fara tsakanin bangarorin biyu, bayan dan wani lokaci sai harsashin yan bindigan ya same shi a cikin sa.

Sai dai duk da haka ya bayyana cewa suma yan bindigan sun samu daman tserewa da raunukan harsasai a jikin su.

An dauki gawar kwamandan da sauran wadanda suka rasa rayukan su zuwa gidan sa dake Toto kana aka yi musu janaza.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An Kashe Kwamandan Yan Banga A Jahar Kogi”