September 2, 2021

An Kama Wata Mata A Kano Bisa Zargin Satar Jarirai A Asibiti

Daga Baba Abdulƙadir
Rahotanni sun tabbatar da cewa an cafke wata mata mai suna Hassana Abubakar mai shekaru 32 yar asalin garin Bauchi da ake zargi ta shigo satar jarirai ne a Asibitin Murtala dake cikin birnin Kano.
Da misalin karfe 1;30 na daren jiya Litinin ne dai hayani ta barke tsakanin Hassana da wata mata da take jinyar mara lafiya, inda bayan da al’umma suka taru sai aka fara tuna nin sata ce ta kawo ta tunda babu sahihin abun da tace tazo yi Asibitin.
kuma tuni aka damkata a hannun hukumar Yan’sanda ta jihar Kano,
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce za su zurfafa bincike domin gano gaskiyar al’amari.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An Kama Wata Mata A Kano Bisa Zargin Satar Jarirai A Asibiti”