An Kama Mutane Fiye Da 40 Bayan Kashe Wani Jami’in Jam’iyyar Dake Mulki A Kasar Habasha

Jami’an tsaron kasar ta Habasha sun sanar da kama mutane 47 saboda zarginsu da hannu wajen kashe jami’i a jamiyyar da take mulki a yakin Amharah.
Sanarwar ta kuma ce, baya ga kisan jami’in an kuma tuhumi mutanen da cewa sun shirya kifar da gwamnatin Aby Ahmad.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka kai wani hari wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar a yankin na Amharah daga cikinsu har da Jirma Yishitil, wanda jami’in jamiyyar da take mulki a yankin.
An kuma sami makamai a tare da mutanen da suka hada bama-bamai da na’urorin sadarwa masu aiki da tauraron dan’adam.
Tashar talabijin din IBC ta kasar Habasha ta bayar da labarin cewa; Dukkanin mutanen da aka kama suna aiki ne daga wata kasa saboda idan sun kwace iko da yankin za su kuma kifar da gwamnatin tarayya.
Yankin Amharah shi ne na biyu mafi girma a kasar Habasha ta fuskar yawan jama’a, kuma ya fuskanci tashe-tashen hankula saboda shirin gwamnati na kwance makaman wata kungiya ta yankin.