September 11, 2021

An Kama Matar Da Ta Saci Jariri A Kano

Daga Muhammad Bakir Muhammad

 

Hukumar yan sanda ta jahar Kano ta bayyana cewa wani bawan Allah da ake kira Sadiq da matar sai Maryam ne suka saci jaririn.

Lamarin ya biyo bayan wani gagarumin shagali da suka shirya don murnar samun ‘Da namiji alhali makobta da abokan arziki sun san cewa Maryam bata da juna biyu.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandan jahar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa hukumar su ta karbi korafin Rabi’u Muhammad wanda shine mahaifin jaririn, wanda yake zaune a unguwar Gayawa dake karamar hukumar Ungogo a Kano cewa daya daga tagwayen da aka haifa masa a ranar ya bata.

Ya bayyana cewa matar sa ta haihu ne a ranar 07/09/2021 a asibitin horarwa ta Muhammad Abdullahi Wase, ya bayyana cewa a lokacin da lamarin ya auku ita mai kula da matar ta sa tana barci a wajen dakin.

Jami’in ya bayyana cewa a bayan da suka karbi korafin ba tare da bata lokaci ba Kwamishinan yan sanda na jahar, CP Sama’illa Shuaibu Dikko ya shirya runduna na musamman kan tsatar da jaririn da kuma kama wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Tuni rundunar ta dakile dukkan shige da fice na asibitin kana kuma suka fara gudanar da bincike amma ba’ayi nasarar samun jaririn ba.

Bayan tsaurara bincike da kuma aiyukan kwararru anyi nasarar kama wata mai suna Maryam Sadiq yar shekara 22 da kuma mijin ta Abubakar Sadiq dan shekara 50 wanda dukkanin su mazauna Rijiyar Zaki ne inda a cikin gidan su aka samu jaririn.

Maryam ta amsa cewa ita ce ta sace yaron daga asibitin Muhammad Abdullahi Wase kuma ta bayyana cewa ta aikata hakan ne bisa tunzurarwar mijin ta wanda ya kasance yana muradin neman ‘Da namiji tsawon shekaru.

Jami’in ya bayyana cewa masu laifin za’a mika su zuwa kotu don hukunci na gaba.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An Kama Matar Da Ta Saci Jariri A Kano”