October 14, 2021

An kama jirgin ruwa dauke da hodar-ibliss a Legas

Daga Balarabe Idriss


Hadakar jami’an tsaron Nijeriya da suka hada da sojojin ruwa, jami’an Kwastam, INTEEPOL, da kuma jami’an hana safarar wayoyi sun yi nasarar cafke wata jirgin ruwa dauke da hodar ibliss da nauyin sa yakai 32.9 kg.

 

Jirgin dai “MV CHAYANEE NAREE” an kama ta ne a kan ruwa na Legas a yayin da take kokarin shigowa kuma sauke Sukari.

Hadakar jami’an dai sun kaddamar da wani aiki na musamman yayin da suka tsaurara tsaro musamman kan kayan da are shigo da su ta kan ruwan, a yayin wannan kokarin ne suka yi nasarar kama jirgin wanda a zahiri an nuna ta ne a matsayin jirgin da ta shigo da Sukari.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An kama jirgin ruwa dauke da hodar-ibliss a Legas”