February 25, 2023

An kai wa jami’an zaɓe hari a Gombe

Wasu da ake zargin ƴan bangar siyasa ne sun kai wa jam’ian zaɓe na wucin-gadi da aka tura wata rumfar zaɓe da ke cikin garin Gombe.

Rahotanni sun ce maharan ɗauke da sanduna da adduna sun ƙwace wa ma’aikatan wayoyi da jakkunansu da wasu kayan aiki.

Haka nan an garzaya da wasu daga cikin ma’aikatan zaɓen zuwa asibiti bayan sun samu raunuka.

Wakilin BBC Hausa na wucin-gadi a Gombe Halilu Mohammed Teli ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare kuma yawancin waɗanda aka kai wa farmakin matasa ne masu yi wa ƙasa hidima.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar ta Gombe ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce sun kama wasu daga cikin maharan sannan sun fara gudanar da bincike kan abin da ya faru.

BBC Hausa ✍️

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An kai wa jami’an zaɓe hari a Gombe”