February 12, 2023

Ba a kai wa Mai Mala hari ba – Gwamnatin Yobe

Gwamnan jihar Yobe da ke arewacin Najeriya Mai Mala Buni ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa yayin yaƙin neman zaɓe a shiyyar Gashua da ke ƙaramar hukumar Bade.

Sai dai gwamnatin jihar Yobe ta musanta Ikirarin tana cewa sai da gwamna ya bar wurin hayaniya ta ɓarke.

Amma gidan Talabijin na ChannelsDubban magoya bayan APC ɗin ne da suka je yakin neman zaɓen suka riƙa yi wa gwamnan ihu suna cewa “ba ma yi, ba ma son Mai Mala Buni”.

An fara rikicin ne lokacin da gwamnan zai miƙa tuta ga ‘yan takarar APC gabanin zaɓen 2023, kawai sai aka fara jifa da dutse da wasu abubuwan na daban.

Sai da aka fitar da Gwamnan daga taron tare da taimakon jami’an tsaro.

Yana yin dai haka ya tilastawa gwamnan da magoya bayansa barin yankin tare da komawa Damaturu ba tare da shiri ba.

Mamman Mohammed wanda shi ne daraktan kula da kafafen yaɗa labari ya ce babu wani abu mai kama da wannan da ya faru.

“Mambarin da ake gudanar da taron ne ya cika, lokacin da Sanata Ahmed Lawal ke bayani, sai aka ce kowa ya sauka kada ya ƙarye, har gwamna da shi sanata.

“Dalilin barin wurin taron da wuri kenan. Muna zuwa wani gidan mai muka ji rikici ya ɓarke tsakanin mabiya jam’iyyar tamu,” in ji Mamman.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ba a kai wa Mai Mala hari ba – Gwamnatin Yobe”