May 29, 2023

​An Kai Harin Yanar Gizo Kan Shafukan Gwamnatin Kasar Senegal

 

Gwamnatin kasar Senegal ta bada sanarwan cewa shafukan yanar gizo na kasar sun dawo suna aiki a jiya Asabr bayan an kai masu hare-hare ta yanar gizo a ranar Jumma’an da ta gabata.

Shafin yanar gizo na labarai Afirka news ta nakalto majiyar gwamnatin na cewa, wadanda suka kai harin sun nuna goyon bayansu ga mutanen kasar Senegal wadanda suke sun a gudanar da zabubbukan masu tsabta a kasar.

 

A ranar jumma’an da ta gabata ne dai babban dan adawa da gwamnatin Makki Sall Usman Sonko ya dawo kasar da sunan ayarin yenci don shiga harkokin zaben kasar wanda za’a gudanar nan gaba.

SHARE:
Labaran Duniya, Rahotanni 0 Replies to “​An Kai Harin Yanar Gizo Kan Shafukan Gwamnatin Kasar Senegal”