January 27, 2024

An Kai Hari Akan Jirgin Ruwan Ingila Dake Dauke Da Man Fetur Zuwa Israila.

Tashar talabijin din ‘almayadin’ mai watsa shirinta daga kasar Lebanon ta bayar da labarin dake cewa; Jirgin ruwan mai dauke da man fetur da aka kai wa hari akan tekun “Red-Sea” yana kan hanyar HKI ne, ba kasar Greece ba, kamar yadda wasu kafafen watsa labaru su ka ambata da fari.

Rahotannin sun ce da akwai jiragen ruwa na yaki guda biyu na Amurka da Birtaniya da suke yi wa jirgin ruwan na dakon man fetur rakiya, sai dai da su ka hango makamin da aka harbo sun janye su ka bar shi, shi kadai.

Shaidun ganin ido sun ce an ga gobara ta tashi a cikin jirgin ruwan da aka kai wa hari.

Kakakin sojan Yemen Janar Yahya Sa’rii ya ce; Sun kai harin ne akan jirgin ruwan Ingila mai dakon man fetur mai suna; “ Marlin Luanda” ta hanyar amfani da makamai masu linzami da su ka dace.

Har ila yau kakakin sojojin na Yemen ya ce za su cigaba da kai wa jiragen HKI da masu kai mata kaya hari, har sai idan an kawo karshen hare-haren da ake kai wa Gaza.

©Hausa radio.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An Kai Hari Akan Jirgin Ruwan Ingila Dake Dauke Da Man Fetur Zuwa Israila.”