March 12, 2023

An Kaddamar Da Rundunar Sojojin Amurka Na Yaki Da Ta’addanci A Afirica

 

Amurka ta samar da rundunar da za ta yaki ta’addanci a nahiyar Afirka a kokarin ganin an shawo kan matsalolin tsaro da suka hana zaman lafiya a wasu kasashen Yammacin nahiyar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Jamus ya bayar da rahoton cewa, Amurka ta kaddamar da rundunar sojin ce da za ta taimaka wajen shawo kan barazanar tsaron da kasashen Yammacin Afirka da dama ke fuskanta daga mayaka masu ikirarin jihadi.

Amurka ta kaddamar da rundunar sojin ce da za ta taimaka wajen shawo kan barazanar tsaron da kasashen Yammacin Afirka ta hanyar gudanar da ayyuka na hadin gwiwa tsakanin sojojinta da kuma sojojin wadannan kasashe.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An Kaddamar Da Rundunar Sojojin Amurka Na Yaki Da Ta’addanci A Afirica”