An kaddamar da Ronaldo a matsayin sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr

Dan wasan kwallon kafa na kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya bayyana a filin taka leda na kulob din Al Nassr a daren jiya Talata, inda aka kaddamar da shi a matsayin sabon dan wasa na Kulob din.
Ronaldo ya amince da tayin da kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr da ke Saudiyya ta yi masa kwanakin baya, inda zai taka leda na tsahon kaka biyu.
Rataba hannu akan yarjejeniyarsa da Al Nassr ta sanya shi ya kasance dan wasan kwallon kafa da ya fi kowanne dan wasa daukar albashi. Kididdigan masana ya nuna cewa Ronaldo zai rika daukar kudi Dala Bakwai ($7) a kowanne dakika (sakan), kana kuma albashin sa a kowanne wata yakai kimanin N245,000,000 (Miliyan Dari biyu da arbain da biyar) a kudin Najeriya.
Tun bayan yarjejeniyar sa da kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr dai shafin kungir ya samu karin sabbin mabiya, inda a cikin kwanaki uku mabiya shafin a shafin sada zumunta na Instagram ya karu daga dubu dari takwas 8k zuwa sama da miliyan 6. Wasu na ganin hakan a matsayin ci gaba ga kungiyar Al Nassr.
Ko kwalliya zai biya kudin sabulu a wannan harkalla ta Ronaldo da Al Nassr? Za mu so jin ra’ayoyin ku.