November 25, 2023

​An Kaddamar Da Kamfe Na Zaben Raba Gardama A Chadi

A yau ne aka fara kamfe na zaben raba gardama kan garambawul a kudin tsarin mulkin kasar Chadi.

An soma kamfe na musamman domin gudanar da kuri’a kan sabon kundin tsarin mulki a kasar, wanda ake ganin hakan zai iya zama zakaran gwajin dafi ga gwamnatin mulkin sojin kasar da kuma zuri’ar Itno da ta shafe shekara 30 tana mulkin kasar.

Shugaban rikon kwarya na mulkin sojan kasar Mahamat Idriss Deby Itno wadda gwamnatinsa ta soma jagorantar Chadi tun daga 2021, ya yi alkawarin mika mulki ga farar hula da kuma gudanar da zabe a bana kafin daga baya ya daga zaben zuwa 2024.

Sama da mutum miliyan 8.3 da ke kasar da ke yankin Sahel aka kira kan su yi zaben raba gardama wanda aka saka 17 ga watan Disamba a matsayin ranar gudanar da shi, wanda wannan wani muhimmin mataki ne wanda zai kai ga zabe da kuma kafa gwamnatin farar hula.

‘Yan adawa da kungiyoyi masu zaman kansu da masana harkokin siyasa sun bayyana cewa wannan zaben ya yi kama da wata hanya wadda ta za tabbatar da Itno da “zuri’arsa” sun ci gaba da mulki bayan shekara 30 suna mulkar kasar

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​An Kaddamar Da Kamfe Na Zaben Raba Gardama A Chadi”