November 24, 2023

An kaddamar da helkwatar shiyya ta MDD a Senegal

Shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya jagoranci kaddamar da helkwatar shiyya ta MDD a birnin Diamniadio mai nisan kilomita 30 daga Dakar, fadar mulkin kasar.

Ofishin wanda aka kaddamar a jiya Alhamis, zai zamo mazaunin hukumomi 34 na MDDr dake Senegal. Kaza lika taron kaddamarwar ya samu halartar mataimakiyar sakatare janar na MDD Amina Mohammed, da shugaban kasar Romania Klaus Iohannis, wanda ke gudanar da ziyarar aiki a Senegal.

 

©cri hausa

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An kaddamar da helkwatar shiyya ta MDD a Senegal”