September 7, 2021

An Hana Sana’ar Chajin Waya A Katsina

Daga Muhammad Bakir Muhammad

Gwamnan jahar Katsina Aminu Hello Masari ya haramta sana’ar chajin wayoyi a kananan hukumomi 19 na jahar.

Yayin kaddamar da kwamiti ta musamman kan karfafa tsaro a jahar ta Katsina don binciken lamarin yan bindiga da masu garkuwa da mutane, Gwamna Masari yace gwamnatinsa daga yanxu zata ji lamarin yan bindigan ta hanyar da ta dace don kawo karshen lamarin rashin tsaro a jahar.

Yace ta dau matakin hana sana’ar chajin wayoyin don fahimtar cewa masu laifin suna amfani dasu wurin samun bayanai musamman wurin wadanda ke kiyayya da kokarin da ake na kawo karshen yan bindigan.

Ya bayyana matakin na hana sana’ar chajin ne a garuruwan da matsalar tsaron yafi shafa, karamar hukumar Jibia, Batsari, Safana, Musawa, Mutazu, Dutsinma, Kurfi, Kafur, Danja, Kaita, Maiadua,Malumfashi, Funtua, Danmusa, Kankara, Sabuwa, Faskari, Bakori da kuma Dandume.

Yayin ganawa da kwamitin, Gwamnan ya basu damar aikin wuce gona da iri muddin suka tsinci kansu a yanayin da ake bukatar yin hakan wurin kawo karshen yan bindigan.
A bayanin shugaban kwamitin kuma kwamishin yan sanda Sunusi Buba, yayi godiya ga Gwamnan ya kuma tabbar masa da yin aiki tukuru don kawo karshen matsalar tsaro a Katsina.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An Hana Sana’ar Chajin Waya A Katsina”