March 20, 2024

An hana bada belin shugaban wata kungiyar addini a Zimbabwe.

 

An hana shugaban wata kungiyar addini a Zimbabwe beli a ranar Talata bayan da aka kama shi a makon da ya gabata bisa zargin cin zarafin yara a lokacin da ‘yan sanda suka gano kananan yara 251 da ke aiki a gonarsa da kaburbura 16.

Ishmael Chokurongerwa da ‘yan sanda suka bayyana a matsayin “annabi mai son kansa” ya bayyana a gaban kotu a garin Norton kusa da Harare babban birnin kasar a ranar Talata tare da wasu ‘yan cocinsa guda bakwai wadanda suma suka fuskanci tuhuma. Ba a nemi su yi roko ba.

Da take hana su beli, alkalin kotun Norton Christine Nyandoro ta ce Chokurongerwa na iya yin amfani da karfinsa wajen tsoma bakin shaidu kuma za a yi zanga-zangar jama’a idan aka sake shi.

An gurfanar da wadanda ake zargin da laifin karya dokar binnewa da kona kone-kone da kuma dokar yara, bayan da ‘yan sanda suka gano yara 251 da suka isa makaranta suna aikin hannu a gonakinsu, da kuma kaburbura 16 da ba a yi musu rajista ba.

Zimbabwe

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An hana bada belin shugaban wata kungiyar addini a Zimbabwe.”