January 28, 2023

An Hallaka ‘Yan Isra’ila 7 A Arewacin Birnin Kudus

Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta sanar da cewa, mutane 7 ne suka mutu yayin da wasu 10 suka jikkata sakamakon wani harbi da aka yi a ranar Juma’a a wani wurin ibadar yahudawa dake a arewacin birnin Kudus.

An kai harin ne a Neve Ya’akov, wani matsugunin Isra’ila da ke gabashin birnin Kudus da ke yankin Larabawa na birnin, wanda gwamnatin yahudawan ta mamaye.

Da misalin karfe 8:15 na dare agogon kasar, maharin dauke da bindiga ya shiga wuta kan jama’a a cikin majami’ar, kafin daga bisani jami’an tsaro sun bindige shi.

Harin dai ya zo ne kwana guda bayan jerin hare haren da Isra’ila ta kai mafi muni cikin shekaru da dama a Yammacin Gabar Kogin Jordan, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane tara tsakanin Alhamis zuwa Juma’a a Jenin.

Kakakin kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas, Hazem Qasem ya bayyana a Gaza cewa, wannan farmakin mayar da martani ne ga laifukan da sojojin mamaya suka aikata a Jenin, kuma martani ne ga laifukan da ‘yan mamaya suka aikata.

Amurka ta yi Allah wadai da abunda ta danganta da mummunan hari, haka shi ma babban sakataren MDD.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An Hallaka ‘Yan Isra’ila 7 A Arewacin Birnin Kudus”