January 22, 2023

An Gudanar Da Zanga-zangar Nuna Kin Jin Fira Ministan Isra’ila Benjamen Natanyaho

 

Dubun dubatan masu zanga’zanga ne suka yi gangami a birnin tel’aviv na Isra’ila domin nuna adawa da sauye-sauyen da suka shafi shari’a da fira ministan israila Benjamin natenyahu ya shirya da ake cece kuce akai,

Gangamin na jiya asabar ji ne mafi girma da aka gudanar tun bayan da fira ministan isra’ila Natanyaho ya sake dawowa kan madafun iko a watan da ya gabata , sama da motane 100,000 ne suka fito kan tituna tare da yin gargadi game da shirin da sabuwar gwamnatin masu tsattsauran ra’ayi take yi na yin gyare-gyare a fannin shari’a, inda suka yi zargin an bullo da shirin don baiwa gwamnatin Karin karfin iko wajen nada sabbin mukamai a bangaren shari’a

Sai dai Natanyaho yayi watsi da zanga-zangar da yanzu haka ta shiga mako na 3 ta nuna rashin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a watan nuwambar shekarar da ta gabata, wanda ya samar da daya daga cikin ministocin masu tsattsauran ra’ayi a tarihin gwamnatin isra’ila

SHARE:
Labaran Duniya, Rahotanni 0 Replies to “An Gudanar Da Zanga-zangar Nuna Kin Jin Fira Ministan Isra’ila Benjamen Natanyaho”