September 15, 2023

An Gudanar da Jarrabawar (PUTME) shiga Jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano a ayau cikin Yanayi Mai kyau.

Shugaban Jami’ar Farfesa Mukhtar Kurawa Wanda Mataimakin Shi Ya wakilce ya zaga ya duba dakunan Jarrabawar Inda ya tabbatar da gamsuwar tsarin Jarrabawar.

Tun Bayan Zamanshi Shugaban Jami’ar yake ta kokari wajen Kara Bude fannuka na Karatu (Department) domin Samun Karin adadin dalibai dake sha’awar shigowa Jami’ar. Don haka zamu cigaba da sake Karo wasu darusan domin Kara diban Dalibai musamman Yan Jihar Kano masu sha’awar shigowa. Muna sake Kara jaddada godiyar mu ga Gwamantin Kano karkashin Eng Abba Kabir Yusuf bisa tallafawa Ilmi da yake ako da yaushe.

 

SHARE:
Labarin CIkin Hotuna 0 Replies to “An Gudanar da Jarrabawar (PUTME) shiga Jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano a ayau cikin Yanayi Mai kyau.”