April 5, 2023

An fara baiwa sojojin Najeriya horo kan dabarun yaki ta hanyar amfani da fasahar sadarwa

A ranar Litinin 3 ga watan nan ne hukumar sadarwa ta tarayyar Najeriya, ta fara bayar da horo kan dabarun yakin zamani ta amfani da fasahar sadarwa, ga daliban sashen nazarin harkokin komfuta, dake kwalejin horas da hafsoshin sojin kasar NDA.

A lokacin da yake shaida yadda horon ke gudana a birnin Abuja, shugaban hukumar Farfessa Umar Danbatta, ya ce yanzu lokaci ya wuce na amfani da tsohon tsarin yaki na gaba da gaba.

Shugaban hukumar sadarwar ta tarayyar Najeriya ya ce gwamnati ta samar da kudade masu yawa, kan wannan sabon tsarin yaki ta amfani da fasahar sadarwar zamani, domin tabbatar da samun dauwamammen zaman lafiya a cikin gida, da kuma kare kasa daga barazanar tsaron daga abokan gaba na waje.

Ya ce duniya ta cigaba ta fuskar fasaha, sannan kuma dabarun fuskantar abokanan gaba ya sauya idan aka kwatanta da yadda aka yi a baya na haduwa da juna kai tsaye ta amfani da manyan makamai.

Farfesa Umar Danbatta ya ci gaba da cewa, shi wannan horo da ake baiwa daliban kwalejin na NDA, ya kunshi yadda ake sarrafa na’urori da aka girke a wasu kebantattun cibiyoyi da aka tanadar a rundunonin soji daban daban dake kasar.

Shugaban hukumar sadarwa ta kasar ya ce irin wadannan na’urori da za a rinka sarrafawa daga gida, za su rinka ankarar da dakarun sojin sama dake fagen fama, maboyar `yan ta`adda ba tare da daukar lokaci ana lalube ba.

Sai dai ya ce ya zama lallai a yi amfani da na’urori ingantattu muddin ana son cimma nasara kan abokan gaba na gida da na waje, a don haka wannan zai zama kalubale babba ga mahukunta.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An fara baiwa sojojin Najeriya horo kan dabarun yaki ta hanyar amfani da fasahar sadarwa”