May 19, 2024

An Dukufa Wajen Neman Jirgin Helikofta Shugaba Ra’isi Da Ya Bata Bayan Hatsari

A Iran an shiga neman jirgin shugaban kasar mai saukar ungulu da ya bata bayan hatsari dauke da shugaban kasar Ibrahin Ra’isi.

Jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari yau Lahadi, kamar yadda gidan talabijin din kasar ya ruwaito.

Daga cikin wadanda suke cikin jirgin har da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir Abdollahian.

Lamarin ya faru ne a lokacin da Shugaban kasar ke kan hanyarsa ta dawowa daga Tabriz, dake arewa maso yammacin kasar, bayan dawowarsa daga kan iyakar kasar da Azerbaijan, inda ya halarci bikin kaddamar da aikin bude wata madatsar ruwa tare da takwaransa na Azerbaijan.

Kawo yanzu masu aikin ceto na ci gaba da kokarin zuwa wurin, amma rashin yanayi mai kyau ya kawo musu cikas.

Ana ci gaba da ruwan sama, sannan hazo ya tirnike yankin.

Daga cikin mutanen da ke cikin tawagar shugaban akwai ministan harkokin kasashen waje, Hossein Amirabdollahian, da gwamnan lardin gabashin Azarbaijan, Malik Rahmati, da limamin Juma’a na Tabriz, Muhammad Ali Al Hashem.

Raisi ya je Azerbaijan da sanyin safiyar Lahadi don kaddamar da wata madatsar ruwa tare da shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev. Dam din dai shi ne na uku da kasashen biyu suka gina a kan Kogin Aras.

Shugaban Sojojin Iran Manjo Janar Mohammad Bagheri ya bayar da umarni ga sojojin kasar da su yi amfani da duk wasu hanyoyin da suke da su wurin taimakawa don gano wurin da hatsarin ya faru

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An Dukufa Wajen Neman Jirgin Helikofta Shugaba Ra’isi Da Ya Bata Bayan Hatsari”