April 1, 2024

An daure dan tsohon shugaban kasar Guinea-Bissau a Amurka bisa laifin safarar miyagun kwayoyi

 

Wata kotu a Amurka ta yanke wa dan tsohon shugaban kasar Guinea Bissau hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa samunsa da laifin jagorantar wata kungiyar safarar tabar wiwi ta kasa da kasa.

Malam Bacai Sanha Jr, mai shekaru 52, ya shirya yin amfani da kudaden da aka samu wajen biyan burinsa na zama shugaban kasar Guinea Bissau ta hanyar juyin mulki, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Shi da ne ga Malam Bacai Sanha, wanda ya jagoranci kasar Afirka ta Yamma daga shekarar 2009 har zuwa rasuwarsa a shekarar 2012.

Ana alakanta Sanha Jr da juyin mulkin da bai yi nasara ba a watan Fabrairun 2022.

An mika shi ga Amurka a watan Agustan 2022, bayan kama shi a Tanzaniya makonni kadan da suka gabata.

An fara shari’ar sa ba da dadewa ba, kuma a watan Satumbar bara, ya amsa laifin hada baki wajen shigo da kwayoyi ba bisa ka’ida ba.

Ana zargin Sanha Jr da shigo da tabar heroin daga kasashe da dama zuwa Portugal, da kuma daga Turai zuwa Amurka.

#GuineaBissau

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An daure dan tsohon shugaban kasar Guinea-Bissau a Amurka bisa laifin safarar miyagun kwayoyi”