An damke matashin da ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da kanwarsa ‘yar shakara 8 a Kano

Hukumar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da damke wani matashi mai suna Gaddafi da take zargi da kisan matar mahaifin sa da kuma kanwarsa ‘yar shekara 8 a daren jiya Asabar da misalin karfe 11:30pm.
Jami’an sun sanar da cewa sun samu rahoton faruwar lamarin ne a daren jiya daga wani da ake kira Sagir Yakubu da ke Fadama a unguwar Rijiyar Zaki da ke karamar hukumar Ngogo a jihar Kano. Malam Sagir ya sanar da jami’an yan sanda cewa a yayin da ya dawo gida ya tarar da gawar matar sa Rabi’atu Sagir ‘yar shekara 25 da ‘yar ta Munawwara Sagir ‘yar shekara 8 cikin jini. Kana kuma ya bayyana cewa yana zargin dan sa mai suna Gaddafi da aikata kisan.
Biyo bayan rahoton, kwanishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Muhammad Dauda ya bada umarni ga wasu rukuni daga cikin jami’ansa karkashin jagorancin DPO na ofishin ‘yan sanda reshen Rijiyar Zaki CSP Usman Abdullahi da ya gaggauta halartan inda lamarin ya faru don mika wadanda abun ya shafa zuwa ga asibiti. Kana kuma ya bada umarnin damke mai laifin ba tare da bata lokaci ba.
Bisa umarnin kwamishina, yan sandan sun garzaya da Rabi’atu da Munawwara zuwa asibitin Murtala sai dai kuma rai yayi halin sa tun kafin isar su.
Wanda ake zargi, Gaddafi Sagir, dan shekara 20 an damke shi a wani kango inda yake kokarin yin hijira daga garin Kano. A yayin bincike, Gaddafi ya amsa laifin sa inda ya bayyana cewa ya yi amfani da sukuldireba ne inda ya caka wa matar maifin nasa a wuya da kuma goshi kana kuma ya shake wuyan kanwar sa Munawwara da dan kwali har sai da ya tabbatar ta daina numfashi.
Ya zuwa yazu ana cigaba da bincike kamar yadda mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Kyawa ya bayyana.
