August 24, 2021

An Dakatar Da Kakakin Majalisar Jihar Kebbi

Daga Muhammad Bakir Muhammad

Rahotanni daga jihar Kebbi na nuna Kakakin majalisar jihar; Hon. Ismaila Abdulmumini Kamba tare da mataimakin sa Alh. Muhammadu Buhari Aliyu an dakatar da su.

Rahoto ya tabbatar da cewa a jumulla ‘yan majalisun 24 ne a yayin da 20 daga cikin su suka goyi bayan dakatarwar.

Tuni dai aka rantsar da sabon Dan majalisa don maye gurbin tsohon kakakin, Muhammad Abubakar Lolo; Dan majilisan da ke wakiltan Bagudo ta yamma shine ya zama sabon kakakin majalisar, a yayin da Muhammad Usman Zuru; Dan majalisa mai wakiltar Zuru ya zama sabon mataimakin kakakin majalisar.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An Dakatar Da Kakakin Majalisar Jihar Kebbi”