October 22, 2021

An cinna wuta fadar wani basarake a jihar Imo

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Wasu mahara da ba’a san ko su wanene ba sun cinna wuta a fadar wani basarake a yankin Etekwuru dake karamar hukumar Ohaji/Egbema na jihar Imo.

Sun hada da lalata wasu kayayyakin da suka kasance mallakin sa wanda suka hada da motar sa kirar Jeep.

Lamarin ya faru a daren Alhamis bayan wata tarzoma da ta barke tsakanin matasan yankin da jami’an soja.

Rikicin dai ya haifar da kisan wani jami’in soja, a bangare guda kuwa sojojin sun kona wasu gidaje a yankin.

A daren Alhamis din ne maharan suka kutsa fadar basaraken inda suke dauke da makamai, a yayin da basu tarar da basaraken ko wani daga cikin iyalansa a gidan ba, sai suka cinna wuta a gidan tare da motar hawan sa.

Rahotanni sun bayyana cewa basaraken ya nemi maboya ne a ofishin yan sanda dake Mmahu don tsira da rayuwar sa.

Ya bayyana cewa shi da mai dakin sa suna cikin gidan a yayin da maharan suka farmaki gidan, sai dai kuma sun yi nasarar tsira da rayukan su.

SHARE:
Rahotanni, Tarbiyyan Yara 0 Replies to “An cinna wuta fadar wani basarake a jihar Imo”