An Cafke Wani Mai Yi Wa Isra’ila leken Asiri a lebanon.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaron kasar Labanon sun cafke wani ba lubane dake aikin leken Asiri ga hukumar lekan asirin isra’ila Mossad ta hanyar daukar hotunan muhimman wurare na kasuwanci da wajen cinkoson jama’a da kuma tattara bayanai kan falasdinaw da ke rayuwa a kasashen larabawa.
Rahoton da jaridar al Akhbar ta wallafa ta bayyana cewa wani mutumin dan shekaru 46 da haihuwa mai suna Farid H ya shiga hannun jami’an tsaro inda ake tsare da shi ana yi masa tambayoyi, mutum mamba ne a jam’iyar labanese political party progressive socialist ne kuma yana karba albashin dala 1000 a duk wata domin gudanar da ayyukan leken asirin,
Wanda ake zargin yayi ikirarin cewa ya aike da sakwanni na neman aiki a shafukan sada zumumta da yawa dake neman ma’aikaci a bangaren da yafi kwarewa, daga bisani ya samu sako daga israila inda suka tura masa kudade domin ya sayi wayar salula , inda da farko sun bukaci ya rike aike musu da lambar jirgin da wasu fasunjoji ke ciki,
©Hausa TV.