October 1, 2023

An Bude Taron Makon Hadin Kai Na Musulmi Karo Na 37 A Iran

A Iran yau ne aka bude babban taron makon hadin kai na kasa da kasa karo na 37 a birnin Tehran, zaman da ke samun halattar manyan baki daga sassa daban daban na duniya.

Shugaban kasar Iran, Ibrahim Ra’isi ne, ya jagoranci bikin bude taron.

A ko wane irin wannan taron yayin zagayowar maulidin haihuwar Manzon Tsira Annabi Muhammad SAW, Iran kan gayyaci jami’an gwamnatocin kasashe, manyan malaman addinin Musulunci da kuma masana da manazarta na duniya, domin yi bayani kan mahimmanci hadin kan musulmi.

Manufar gudanar da zaman taron tsakanin mazhabobin Musulunci ita ce shimfida matakan samar da hadin kai da taimakekkeniya tsakanin al’ummar musulmi da irin rawar da malamai zasu taka a fagen samar da kusancin ra’ayi a fannonin ilimi musamman a bangaren ilimin fikihu, usulu, akida, tafsirin alkur’ani da sauransu, kamar yadda zaman taron ke tattauna al’amuran kasashen musulmi da matsalolin da ke addabar musulmi da neman hanyar warware su.

Musulinci na bukatar hadin kai tun fil-azal, kuma hakan na karuwa yau da kulun, inji shugaban aksar Iran, Ibrahim Ra’isi, wanda ya taya al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayen halitta, (SAWA).

©Htv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An Bude Taron Makon Hadin Kai Na Musulmi Karo Na 37 A Iran”