August 23, 2023

An Bude Taron BRICS Karo Na 15, Bisa Taken “BRICS da Afirka”

An bude taron kasashen BRICS, karo na 15, a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu.

Maudu’in taron karo na 15 shi ne “BRICS da Afirka”

Kasashen na BRICS wadanda suka hada da Brazil, da Rasha da Indiya da China da Afirka ta Kudu, su ke da kashi daya bisa hudu na tattalin arzikin duniya.

An kara tsaurara tsaro a birnin inda Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya karbi bakuncin Shugaba Xi Jinping na China da Firaiministan Indiya Narendra Modi da Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva da kuma wasu shugabannin Afirka 50.

Shugaban Rasha Vladimir Putin, wanda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ke nema ta kama shi kan zargin laifukan yaki a Ukraine, ba zai halarci taron ba sai dai ya wakilta ministan harkokin wajen kasar Sergie Lavrov.

Kasashen, wadanda suke da kashi 40 cikin 100 na jama’ar duniya, na da ra’ayin bai-daya na tsarin duniya da suke ganin zai fi nuna muradunsu da samun daukaka.

©VOH

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An Bude Taron BRICS Karo Na 15, Bisa Taken “BRICS da Afirka””