September 20, 2023

An Bude Babban Taron Zauren MDD, Karo Na 78 A New York

 

An bude taron Majalisar Dinkin Duniya, karo na 78 a birnin New York na Amurka.

A jawabinsa na bude taron, babban sakataren MDD, Antonio Guterres, ya nuna damuwa game da sauyin yanayi dake addabar duniya, wanda ke Haifar da bala’I iri daban daban.

Mista Guteress, ya jajanta game da bala’in ambaliyar ruwa na Derna, a Libya, daya daga cikin misalai na sauyin yanayi.

Taron na MDD, shi ne wanda yake hada kasashe 193 a wuri guda a kowane watan Satumba.

A cikin jawabinsa, shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya bukaci tattaunawa don kawo karshen yakin da ake yi a Ukraine.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, zai yi jawabi karon farko a zauren na MDD.

Babbar tattaunawar za ta gudana ne daga 19 zuwa 23 ga watan Satumba, kuma a ci gaba da shi a ranar 29 ga watan na Satumba.

A lokacin wannan tattaunawa wakilan dukkanin kasashe masu wakilci a Majalisar ta Dinkin Duniya za su yi bayani kan abubuwan da suke damun su.

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “An Bude Babban Taron Zauren MDD, Karo Na 78 A New York”