May 25, 2023

Amurka Ta Yi Barazanar Kakaba Takunkumi Ga Masu Rikici A Sudan.

Amurka ta yi barazanar kakaba takunku kan bangarorin dake rikici a Sudan, muddin basu mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma ba.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya bukaci bangarorin dasu mutunta yarjejeniyar ko kuma su fusknaci takunkumi.

Blinken, ya ce, ‘’fadan ba shi da wata fa’ida, illah kawai wargaza kasar’’.

Wanann dai an zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun janar-janar dake rikici a kasar.

Tun da farko dai kafin hakan Kasashen Saudiyya da kuma Amurka, sun bukaci bangarorin dake rikici a Sudan dasu mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Amurka Ta Yi Barazanar Kakaba Takunkumi Ga Masu Rikici A Sudan.”