August 29, 2021

Amurka : Har Yanzu Akwai Babbar Barazana A Filin Jirgin Saman Kabul

Daga Hausa Radio Iran

Shugaban Amurka Joe Biden, ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar fuskantar sabon hari cikin sa’o’I 24 zuwa 36 a filin jirgin saman Kabul.

Da yake sanar da hakan ranar Asabar, bayan ganawa da mashawartansa kan harkokin tsaro, Mista Biden, ya kara da cewa, har yanzu akwai babbar barazana da kuma yiwuwar fuskantar hare haren ta’addanci a filin jirgin saman na Kabul.

Game da harin da Amurka ta kai a gabashin Afghanistan kuwa inda ta kashe wasu mambobin kungiyar IS biyu, shugaba Biden, ya ce harin ba zai zamo na karshe ba.

A harin ta sama data kai jiya Asabar, rundunar sojin Amurka ta ce, ta hallaka wani jigon kungiyar IS da ya kitsa yadda aka kai harin filin jirgin saman Kabul.

Harin kunar bakin waken na ranar Alhamis ya kashe mutun 170 da suka hada da sojojin Amurka 13

 

SHARE:
Tarbiyyan Yara 0 Replies to “Amurka : Har Yanzu Akwai Babbar Barazana A Filin Jirgin Saman Kabul”