Amurka BaTa Cancanci Matsayi A Kwamitin Kare Hakkokin Dan Adam Na MDD Ba

Jakadan kasar Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa a birnin Geneva Ali Bahreini ya ce; Amurka da ke da bakin tarihi kan batun kare hakkin bil’adama ba ta cancanci matsayinta a hukumar kare hakkin bil’adama ba.
Ali Bahreini ya bayyana hakan a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Asabar, a matsayin martani ga kalaman da jakadan na Amurka ya yi kan Tehran, wanda zai jagoranci kwamitin kare hakkin bil adama na MDD.
Ya dora wani faifan bidiyo a shafinsa da ke nuna wasu shari’o’i na laifukan hakkin bil’adama na Amurka, ciki har da harbo jirgin saman fasinja na Iran da makamaki mai linzami, wanda wani jirgin ruwan yaki na sojojin ruwan Amurka ya yi a kan gabar ruwan kasar kasar Iran da ke gabar tekun Farisa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 290.
A ranar 3 ga Yuli, 1988, jirgin ruwan yaki na USS Vincennes ya harba makami mai linzami kan jirgin saman Iran Airbus A300B2 da ke tafiya a sararin samaniyar mashigar Hormuz daga tashar jiragen ruwa ta Bandar Abbas zuwa Dubai, dauke da fasinjoji 274 da ma’aikatan jirgin 16, inda dukkaninsu suka rasa rayukansu