November 23, 2023

Amnesty Ta Ce Isra’ila Ta Aikata Laifukan Yaki A Gaza

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta ce Isra’ila ta aikata laifukan yaki a zirin Gaza.

Amnesty ta kafa hujja da wasu hare-haren bama-bamai guda biyu a da Isra’ilar ta kai a Gaza, a ranakun 19 da kuma 20 ga watan Oktoba, wanda ya kashe fararen hula 46 ciki har da yara 20.

A rahoton data fitar jiya Litini, Amnesty, ta ce bama-baman sun afkawa wata majami’a da daruruwan fararen hula da suka rasa matsugunansu ke samun mafaka a birnin Gaza.

Kungiyar ta ce ta samu ziyartar wurin da lamarin ya shafa, ta kuma dauki hotuna bayan harin bama-baman, sannan ta yi magana da mutane 14 da suka hada da wadanda suka tsira da rayukansu da kuma wani dan uwan wadanda abin ya shafa.

Ta ce ta nazarci hotunan tauraron dan adam wajen gano wuraren da kuma tabbatar da wadannan hare-haren.

 

©V.OH

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Amnesty Ta Ce Isra’ila Ta Aikata Laifukan Yaki A Gaza”